28/10/2017
MAI ALFARMA SARKIN MUSULMI ALH MUHAMMAD SA'AD ABUBAKAR 111 YA KARRAMA MALAM YA'U DANDA A FADARSA.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh Muhammad Sa'ad Abubakar 111 Ya karrama Malam Ya'u Mohammad Danda da shedar MALANTA. Shedar wadda tasami halartar Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto Alh Ahmad Aliyu da tawagarsa. Wannan ya faru ne lokacin gaisuwar ta'aziyar Wazirin Sokoto.
A jawabin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Yace" Ina sheda muku na tabbatar da Malam Ya'u A matsayin Malami daga yau wanda zai kirashi, ya kirashi MALAM YA'U DANDA na soke ku kirashi da sunan Honourable ko S A ko Alhaji, A'A kukirashi MALAM YA'U na tabbatassai. Sarkin Musulmi Yace ga kyauta inbaka kaje ka duba ka kara ilimi.
Mai Martaba Ya bashi wani littafi na jawabbanda yayyi wajan tarukka cikin Nigeria da wasu kasashen duniya.
Allah Ya kara Daukaka Mal. Ya'u Mohammad Danda, Ya Kara Yimishi Jagora. Muna Taya Shi Murna.
27/10/2017.